1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amr Mussa ya yi wa majalisar al´umar Kurdawa jawabi

October 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvOB

A jawabin da ya yiwa majalisar al´umar Kurdawa, babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Amr Mussa ya yi kira da kafa wata kasar Iraqi mai ´yan´uwantaka da kuma hadin kai tsakanin al´umominta. Lokacin da yake magana a gaban wakilan majalisar dake birnin Erbil na arewacin Iraqi, Amr Mussa ya sake jaddada muhimmancin dake akwai wajen shirya taron sasantawa tsakanin ´yan shi´a da sunni da kuma Kurdawa kamar yadda kungiyarsa ta ba da shawara. A jiya asabar babban malami ´yan shi´a a Iraqi Ayatollah Ali Al-Sistani ya nuna goyi da bayan shirya wannan taro.