1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwear siyasar Amurika a gabas ta tsakiya

Sadissou YahouzaFebruary 19, 2009

Barack Obama ya bayyana yin iya ƙoƙarinsa domin warware rikicin gabas ta tsakiya

https://p.dw.com/p/Gxa0
Siyasar Obama a gabas ta tsakiyaHoto: AP / DW


Sabon shugaban ƙasar Amurka Barak Obama yayi alƙawarin yin bakin ƙoƙarinsa wajen cimma zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya. To sai dai kuma ba wanda ke sa ran cimma nasara a cikin gaggawa, ganin mawuyacin halin da ake ciki a wannan yanki. Amma fa fadar mulki ta White House ba ta fid da ƙauna ba cewar ko ba-daɗe ko ba-jima kwalliya zata mayar da kuɗin sabulu

Amsoshin biyu ne ƙwararrun masana a birnin Washington kan bayar a game da tambayar abin da ya banbanta manufofin ƙetare na gwamnatin Obama da ta Bush. Da farko abin da ya danganci Rasha da Asiya da yankunan rikici na Irak da Afghanistan da kuma dangantaka da ƙasar Iran za a samu sauyin manufofin matuƙa ainun, a ɓangare guda, amma a ɗaya ɓangaren ba za a samu wani canji na a zo a gani ba a manufofin Amurka dangane da yankin gabas ta tsakiya da kuma abin da ya shafi Isra'ila da Palasɗinawa.

Ko shakka babu cewar George Mitchell da Obama ya naɗa a matsayin wakilin musamman a yankin mai fama da rikici ƙwararren jami'in diplomasiyya ne kuma za a samu canjin murya a dangantaka da sassan biyu da basa ga maciji da juna, amma fa ba wani abin da zai biyo bayan hakan. Za a ci gaba da fama da ɗawainiyar neman ɗinke ɓarakar da ake fama da ita tsakanin Isra'ila da Palasɗinawa. Kuma a can birnin Washington ba mai tsammanin cewar za a samu wani canji a cikin ƙiftawa da bisimilla. Aƙalla dai sabon shugaban na Amurka ya aika da kyakkyawan saƙo ga Isra'ila da duniyar Musulmi tun a farkon wa'adin mulkinsa. Dangane da fadar mulki ta Tel-Aviv dai Obama cewa yayi:Tsaron lafiyar Isra'ila nauyi ne da ya rataya a wuyan Amurka. Ba zamu darara ba muna masu ba wa Isra'ila goyan baya akan 'yancinta na kare kanta daga kowace barazana. An yi shekaru da dama Hamas na harba dubban rokoki akan al'umar Isra'ila da ba su san hawa ba su san sauka ba. Babu wata demoƙraɗiyyar da zata yarda da irin wannan barazana ga al'umarta.

To sai dai kuma shugaban na Amurka bai yi watsi da makomar Palasɗinawa ba, inda ya lokacin hira da tashar telebijin ta Al-Arabiya tayi da shi yake cewar:Alhakin da ya rataya wuyana dangane da duniyar musulmi shi ne in bayyana musu a fili cewar Amurkawa ba abokan gabarsu ba ne. Mun kan tabka kurakurai kuma mu ba mu cika goma ba. Amma abu ɗaya dake akwai shi ne mu ba wata daula ce ta mulkin mallaka ba. Abin da zan faɗa muku shi ne, bana ganin akwai wani dalilin da zai hana mu sake farfaɗo da nagartacciyar dangantakar da ta wanzu tsakaninmu misalin shekaru 20 zuwa 30 da suka wuce. Bugu da ƙari kuma ba magana ta ce mizanin da za a auna ni da shi ba, sai dai aikina.

A yanzun dai ba abin da ya rage illa a sa ido a ga irin rawar da wakilin musamman da Obama ya naɗa akan rikicin yankin gabas ta tsakiya George Mitchell zai taka a cikin watanni masu zuwa. An dai saurara daga bakinsa yana mai cewar:

Mutane su ne mafarin rikici kuma sune ke da ikon kawo ƙarshensa. Na ga yadda lamarin ya kasance a Irland ta arewa, ko da yake wajibi ne na haƙiƙance cewar abin ya ɗauki lokaci mai tsawon gaske.