1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AMURKA DA KAWO CIKAS A HARKAR TAIMAKO

August 3, 2004
https://p.dw.com/p/BvhZ
DAYA DAGA CIKIN YARAN KASAR AFGHANISTAN DIN DAKE CIKIN BUKATAR TAIMAKO
DAYA DAGA CIKIN YARAN KASAR AFGHANISTAN DIN DAKE CIKIN BUKATAR TAIMAKOHoto: AP

An yi kakkausar suka akan Amurka da Britaniyya, akan yadda lamurran bayar da agaji ke dagulewa, a kasar Afghanistan.

Kungiyar bada agaji ta duniya, ta Oxfam, tayi kakkausar suka, akan yadda wadannan kasashen ke aikin son rai, a kasar Afghanistan, a inda maimakon su taimaka waje rarraba kayan taimako, kamar yadda ya dace ga mutanen dake cikin matukar bukata, wadanda suke cikin halin matsi, a kasar Afghanistan, sai suna karkata ga cimma wasu bukatu nasu. Amurka, dai tayi kane kane, ta kakkare rabon kayan agajin. Maimakon ta bari kungiyoyin bayar da agaji kamar kungiyar Oxfam din suyi, aikinsu a bisa adalci kamar yadda aka san anayi, sai Amurkar, tare da kawarta Britaniyya, suka zamanto, suna ta karkata bayar da taimako

ga masu basu bayanai na sirri kurum, suna yin watsi da ainihin mutanen da sune, ainihin mabukata, a cikin kasar Afghanistan din. A halin da ake ciki dai, mutanen kasar sun kasa rarrabewa, tsakanin masu basu agaji na kungiyoyin taimako na duniya, da sojojin taron dangi a kasar. Amurka dai, ta tsaya kai da fata cewar, bawai kungiyoyin bada agaji na duniya, ne kawai, keda alhakin samarda kayan taimako da rarrabasu, a cikin kasar ba, sojojin taron dangi na Amurkar da Britaniyya, da Faransa, da Italiya, dana Jamus, dana sauran kasashe na Austaralia, da Canada da Belgium, da Denmark, da Norway da Jordan, dake cikin sojojin taron dangi, na cikin wannan aikin.

Kungiyar Oxfam, dai tace, matakin da Amurka ke dauka, wanda baya kan hanya, na bani bayanin sirrin kana-in-baka-taimako, a kasar Afghanistan, shine ma ya sanya, tun a bara, kungiyar bada agaji ta Oxfam din, ta dakatar da aikinta, a Kandahar, inji Caroline Green, ‘yar wannan kungiyar.

Itama kungiyar nan ta bada agaji ta Medecins sans Frontieres, wadda ake kira MSF a takaice, ko kuma, Doctors Without Borders, wadda ta shafe kusan shekaru 24, cur, tana ta gudanar da ayyukan taimako, a kasar Afghanistan, da ma’aikata 80 na waje da 1,400 na kasar Afghanistan, tace, daga cikin dalilan janyewar ta data kammala a satin daya gabata, daga cikin kasar Afghanistan din, bayaga batun dagulewar harkokin tsaro, inda ake ta kashe mata mutane, babban lamarin shine, yadda sojojin Amurka, sukeyi katsalandan, suna yin ruwa da tsaki, a harkokin rarraba kayan agaji ga jama’a a kasar Afghanistan, a inda suke bada taimakon kurum, ga wadanda suka basu bayanai, alhali sauran jama’a, ana barinsu a cikin wahala, ta babu gaira babu dalili.

Sauran kungiyoyin bada agaji na duniya ma, dake gudanarda ayyukansu, a kasar Afghanistan, suna ta kokawa, akan shigar shigular da Amurka, keyi masu, akan aikin da sune, suke da alhakinsa. Michael Neuman, na kungiyar MSF, dai yace, Amurka bata da wani nufi, a cikin wannan harkar, in banda ta cimma, burinta na siyasa da harkokin kara baza karfin sojinta, a cikin wannan kasar ta Afghanistan. Ya kara da cewar, aikin son rai, a harkokin bada agaji, bashi cikin ka’idojojin dake shinfide, na zamantakewa na duniya. Yace babu wani mazauni a inda ake hada harkokin siyasa da batun bada taimako, a ko ina, a duniya.

ABUBAKAR D. MANI