1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka da sansanin Guantanamo

May 16, 2006
https://p.dw.com/p/BuyH

Hukumar tsaron Amurka ta Pentagon, a karon farko ta baiyana sunayen dukannin mutanen da ake tsare da su a sansanin Guantanamo dake Cuba tun bayan da aka bude sansanin a watan Janairu na shekara ta 2002. Kakakin hukumar yace jadawalin sunayen ya kunshi mutane 759 da kuma usulin kasashen su. A halin da ake ciki sansanin na dauke da fursunoni 480, yayin da kuma fursunoni 272 walau dai an sake su ko kuma an mika su ga kasashen su na haihuwa. Fursunoni goma ne kacal aka tuhume su a kotu kuma babu koda mutum guda da aka kammala shariár sa.