1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta rubanya kason kudi domin yaki da taáddanci a nahiyar Afrika

A. T. BalaFebruary 16, 2006

Shaáwar da Amurka ke da shi a nahiyar Afrika ba, kawai kasancewar yan al-Qaída ko yan taádda ba ne a yankin, sai don fadada daular ta, da kuma manufar ta bunkasa matakan tsaro.

https://p.dw.com/p/Bu1f
Shugaban Amurka George W Bush
Shugaban Amurka George W BushHoto: AP

Yayin da gwamnatin Amurka ke kara dogaro da albarkatun mai da Allah ya huwacewa nahiyar Afrika, manazarta alámuran yau da kullum na ganin cewa nahiyar zata cigaba da daukar hankali musamman bisa laákari dakarun sojin Amurkan a kasashen na Afrika da kuma kasancewar kungiyoyin yan takife musulmi masu tsananin kishin Islama a wananan yankin. A zancen da ake yanzu, kasashen Afrika su ne ke samar da kashi goma sha biyu cikin dari na daukacin man da Amurka ke bukata a shekara, kuma ana ganin nan da shekaru 10 zuwa 15 masu zuwa, man da kasashen Afrikan zasu rika samarwa ga Amurka zai rubanya zuwa kashi 25 cikin dari. Bayan harin 11 ga watan Satumbar shekara ta 2001 da kuma yake yake biyu da Amurkan ta jagoranta a gabas ta tsakiya, wato a kasashen Iraqi da Afghanistan, akwai alamun cewa manyan kamfanonin mai hade da shugaban Amurka George W Bush na da matukar shaáwa ga albarkatun karkashin kasa dake jibge a yankin Niger Delta da Gulf of Guinea da kuma wasu kasashen Afrika dake yankin Sahel.

A shekarar data gabata, kasar Amurka ta kebe kudi dala miliyan 16 wanda bai taka kara ya karba ga shirin yaki da taáddanci a yankin Sahara, idan aka kwatanta da abin da ta ke kashewa a kutsen da tayi a wasu sassa na duniya. A bana gwamnatin ta kara yawan kudade domin yaki da taáddancin a nahiyar Afrika ya zuwa dala miliyan 31, inda kuma ta ke fatan zuwa shekara ta 2008 za ta rubanya kason da zata warewa wannan yanki ya zuwa dala miliyan 100 bayan duk shekaru biyar.

Ga masu nazarin yadda alaámura ke gudana, tambayar da suke ita ce, shin ko kasar ta Amurka na da niyar kara yawan dakarun sojin ta a nahiyar ta Afrika ne? Amsa dai ita ce babu wannan shiri a cewar manjo Holly Silkman jamiar hulda da jamaá a rundunar sojin Amurka na nahiyar turai dake Stuttgart a nan Jamus. Baya ga kasashen yammaci da tsakiyar turai, Amurka na kuma Ikrarin iko na kariya da samar da tsaro a yammaci Afrika. Silkman ta ce ko da yake babu wani shiri na tura dakarun sojin Amurka zuwa nahiyar, a hannu guda suma kasashen na Afrika babu wacce take maraba da sojojin a yankin kasar ta. Sai dai a waje guda akwai yan kalilan din sojin Amurkan wadanda suka nufi arewa maso yammacin Afrika inda suke atisayen bada horo akan yaki da taáddanci bisa hadin gwiwa da sojojin Chadi da Nigeria da Mauritaniya da kuma wasu kasashe. Hakazalika,akwai shirin bada horon yaki da taáddanci a tsakanin Amurka da kasashen Ghana da Morocco da gabon da kuma Senegal .

Silkman ta kara da cewa suna da masaniya a game da wasu sansanonin bada horo a yankin na Afrika wadanda yan taádda ke amfani da su don kaifafa dabarun su na taáddanci, tace gwamnatin Amurka a shirye take ta taimakwa kasashen Afrika idan suka bukaci hakan . To amma a hannu guda wasu manazarta na masu raáyin cewa fiye da shekaru 60 da suka wuce akwai musulmi masu tsatsauran raáyi na addinin Islama a yankin na Sahel amma baá taba danganta su da wata tarzoma ta nuna kyama ko adawa da yammacin turai ba. Jamia´n Amurka sun ki fayyace manufar da Amurkan take da shi musamman a gabas maso yammacin Afrika ba, amma wani tsohon jamiín maíaktar harkokin wajen Amurka yace ya yi Imani samun angizo na sojin Amurka a arewa maso yammacin Afrika, wata alama ce dake nuni da cewa Amurka na karfafa huldar ta da wadannan kasashe, sai dai ya baiyana damuwa cewa ba ya tsammani akwai wata tattaunawa sosai tsakanin Amurkan da shugabannin addinin Islama a yankin na Afrika.