1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta yabawa ƙoƙarin Syria na daƙile yunƙurin harin taáddanci

September 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bujg

Gwamnatin ƙasar Syria ta fara bincike domin gano waɗanda suka shirya kai harin da bai yi nasara ba a kan ofishin jakadancin Amurka dake birnin Damascus. Mutum uku yan ƙunar baƙin wake da wani jamiín tsaro na ƙasar Syria, sun rasa rayukan su a yayin musayar wuta a lokacin da yan kunar bakin waken suka yi yunƙurin afkawa ofishin jakadancin. Ministan alámuran cikin gida na ƙasar Syria Bassam Abdel Majid yace ɗaya daga cikin yan bindiga daɗin da aka kama na bada haɗin kai ga jamián bincike.

Amurka ta yabawa gwamnatin Syria bisa ɗaukar mataki cikin gaggawa na ganin harin bai cimma nasara ba. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta ce ta yi Imani mahukuntan Syrian sun yi namijin ƙoƙari wajen ƙare rayukan Amurkawa kuma abin a yaba ne. Dangantaka tsakanin Syria da Amurka ta yi tsami a game da yaƙin Iraqi dana Lebanon da kuma marawa yan takifen falasɗinawa baya waɗanda ke adawa da ƙasar Israila.