1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta yi kira da a binciki zargin magudi a zaben Rasha

December 3, 2007
https://p.dw.com/p/CWP5

Gwamnatin Amurka ta yi kira ga hukumomin Rasha da su yi bincike kan zargin maguɗi a zaɓen da aka gudanar.Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka ta White House Dana Perino tace rahotanni daga Rasha sun baiyana cewa an tafka maguɗi a zaɓen.Kodayake tace ba zasu yanke hukunci kan zaɓen ba. Jamiyar Putin ta United Russia Party ta lashe zaɓen majalisar wakilai da kashi biyu bisa uku na kuri`u da aka kaɗa wanda ya baiwa magoya bayan Putin damar aiwatar da canje canje cikin kundin tsarin mulkin ƙasar.