1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka tace ba zata tattauna kai tsaye da Iran ba.

November 28, 2006
https://p.dw.com/p/BuZv

Kasar Amurka tace ba zata tattauna kai tsaye da Iran ba har sai kasar ta dakatar da inganta uraniyum da take yi.

Shugaba G.Bush na Amurkan a ziyarar da ya ki Estonia yace kasarsa tana goyon bayan tattaunawa tsakanin Iran da makwabtanta amma ba da Amurka ba kai tsaye muddin dai taci gaba da wannan shiri.

Bush yana kann hanyarsa ce ta zuwa taron shugabannin kungiyar tsaro ta NATO a Latvia.

An dai zargi Iran da Syria ta kara hura wutar rikici a Iraq,ana kuma ganin cewa Amurka zata bukaci tattaunawa da kasashen biyu a kokarin da take yi ido a rufe na ganin an kare Iraq fadawa yakin basasa.

Sai dai tuni jamaa da dama sun baiyana cewa kasar ta Iraqi ta rigaya ta tsunduma cikin yakin basasa,

haka shima sakataren MDD Kofi Annan yace muddin dai ba a gaggauta kawo karshen zubda jini ba kasar tana gab da fadawa mumunan hali fiye da yadda ake zato.