1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AMURKAWA A IRAQI SUN FARA FUSKANTAR WULAKANCI.

April 2, 2004
https://p.dw.com/p/Bvku

A yayin da fadar white House ta Amurka ta dukafa ka in da nain wajen kare zarge zargen da ake mata bisa yakin kasar iraqi,musanmamma bisa kusantowar zabe na shugaban kasa,sai gashi kwatsam a jiya litinin wasu yan fadan sari ka noke sun harbe wasu yan kwangila na Amurka kusan guda goma sha 18 tare da jan gawarwakin su a kasa titi izuwa titi a cikin garin Falluja na kasar iraqi.

Wan nan irin wulakanci da Amurkawan suka fuskanta,wanda kuma kafafen yada labarai na duniya suka dinga nunawa tare da buga hotunan a jaridu ya harzuka fadar da white House da kuma gwanatin rikon kwarya ta Iraqin.

Bugu da kari wan nan al,amari a cewar rahotanni da suka iso mana ya faru ne a dai dai lokacin da wasu yan fadan sari ka noken suka yi sanadiyyar mutuwar wasu sojin Amurka biyar a lokaci guda ta hanyar saka musu bom a tsakiyar hanyar da motar take bi.

Bugu da kari rahotanni sun shaidar da cewa a tun lokacin da dakarun hadin gwiwa da kasar Amurka kewa jagoranci suka kifar da gwamnatin Saddam Husssin,Tawagar hadin gwiwar ke fuskantar hare haren kunar bakin wake da kuma na kwanton bauna.

To Amma babban abin takaici a cewar bayanai da suka iso mana shine na yadda ire iren wadan nan hare hare ke kara kazanta a kullum ranar allah taalah.

A waje daya kuma bayanai sun tabbatar da cewa irin wan nan wulakanci da wadan nan mutane na Amurka suka fuskanta a garin na falluja,irin sane ya faru kann sojin kasar ta amurka a somalia,wanda hakan shiya haifar ala dole gwamnatin ta Amurka ta jaye dakarun nata daga wan nan kasa.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa babu yadda mutanen kasar ta Somalia basuyi ba don ficewar dakarun sojin na Amurka daga kasar a wan nan lokaci amma abu yaci tura,to amma sakamakon daukar irin wan nan mataki daya faru a garin na falluja Ala dole suka fice.

Bisa hakan a cewar tsohon wakilin mujjallar New York Times,John Burns, bisa sabon salo da yan fadan sari ka noken na kasar ta iraqi suka fito dashi a yanzu haka ya zama wajibi mahukuntan na Amurka su kara tunani naci gaba da girke dakarun su a kasar ta Iraqi.

A daya hannun kuma wani tsohon jamii a hukumar tsaro ta Pentagon,Lawrence Korb cewa yayi irin wan nan halin da wadan nan jamiiai suka fuskanta a kasar ta iraqi,babu shakka ya tuna masa irin halin da sojin kasar suka samu kansu a ciki a kasar vietnam a lokacin mulkin Ronal Reagan.

A waje daya kuma bayanai sun nunar da cewa a yayin da kasar ta Amurka bisa taimakon mdd ke gudanar da tsare tsaren mika mulki ga yan kasar ta iraqi a karshen watan yuni na wan nan shekara da muke ciki, sai gashi a daya hannun kuma rigingimu a tsakanin kabilun kasar na kara tsamari wanda hakan shima ya kara taimakawa wajen kara yamutsa harkokin siyasar kasar.

A yanzu haka dai a cewar masu nazarin abin da kaje yazo na gabas ta tsakiya zabi ya ragewa mai shiga rijiya,musanmamma ga kasar ta Amurka nata gaggauta daukar matakin janye sojin ta daga kasar ko kuma suci gaba da fuskantar wulakanci,kamar yadda bayanai suka fara nunawa.

Bisa kuwa irin abin da ya faru a kasar ta iraqi kann Amurkawan tuni gwamnatin Amurka da kuma ta rikon kwarya dake kasar ta iraqi taci alwashin sai ta nemo wadan da keda hannu a cikin gudanar da wan nan kisa tare da wulakanci don gurfanar dasu a gaban kuliya.