1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Anƙi baiwa General Motors agaji

June 10, 2010

Izuwa yanzu kamfanin GM ya kasa samun nasara, bisa buƙatar samun tallafi daga Jamus

https://p.dw.com/p/Nmh3
Shugaban kanfanin GMHoto: AP

Gwamnatin ƙasar Jamus ta yi watsi da neman agajin da kamfanin ƙera motoci na General Motors ya yi, inda yake buƙatar samun tallafin gwamnati daga Jamus domin agazawa rashensa dake Turai, wato kamfanin ƙera motoci na Opel. Ministan kula da tattalin arziki na Jamus Rainer Bruedele yace kamfanin Opel ya samu agaji dai dai kima. Duk haka dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tace za ta gana da jami'an jihohin da ake ƙera motocin, don tattauna batun a matakina na jihohi. Kamfanin Opel dai yana da ma'aikata kimanin dubu 25 a  ƙasar ta Jamus, kana kamfanin na GM ya nemi tallafi daga gwamnatin Jamus har na fiyeda euro biliyan ɗaya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammad Nasiru Awal