1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ƙulla sabuwar dangantaka a tsakanin Nahiyar Turai da Afrika

Ibrahim SaniDecember 10, 2007
https://p.dw.com/p/CZYK

Shugabannin ƙasashen Turai da na Afrika sun cimma yarjejeniyar haɗin kan tattalin arziki a tsakaninsu. An cimma hakan ne a ƙarshen taron ƙolin da su ka gudanar ne jiya lahadi a birnin Lisbon na ƙasar Portugal. Taron dake a matsayin irinsa na biyu a tsawon shekaru bakwai ya samu halartar shugabanni sama da 67 daga Nahiyoyin biyu. A lokacin da take jawabi, shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta soki shugaban Zimbabwe game da batun take hakkokin bil adama. Hakan a cewar Merkel abune dake lalata ƙimar Afrika baki ɗaya a idon Duniya. To sai dai a waje ɗaya Angela Merkel ta nu na gamsuwa game da taron ƙolin. Da yawa dai daga cikin shugabannin Afrika sun yi watsi da ƙudurin cinikayya da Ƙungiyyar Eu ta gabatar a taron. Ƙudurin a cewar rahotanni bai bawa manoman Afrika dai-daito da takwarorinsu na Nahiyar ta Turai ba.