1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ɗage gangamin adawa a Kenya

Zainab MohammedJanuary 3, 2008

Yunkurin gangami ya haifar da rikicin kone kone

https://p.dw.com/p/Cjps
Gamgamin adawaHoto: AP

Jamiiyyar adawa ta ODM dake karkashin jagorancin Raila Odinga,ta sanar da ɗage zanga-zangar lumana da aka shirya gudanarwa a Kenya yau,domin nuna adawa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a makon daya gabata.

Wani babban jamiin jamiyyar ta Odinga, William Ruto ya bayyanawa gangamin waɗanda suka fito domin gudanar da zanga-zangar a tituba Nairobi cewar a ranar talatan mako mai zuwa ne 8 ga wannan watan ne zasu sake haɗewa a filin ‘yanci na Uhuru dake Nairobin.

Ayau nedai jamm’iyyar adawar ta kira gangamin mutane million guda domin nuna adawa da sakamakon zaɓen daya sake bawa shugaba Mwai Kibaki madama iko a wannan ƙasa mai karfin tattalin arziki dake yankin gabashin Afrika.

Jami’an tsaro dai sunyi arangama da da magoya bayan yan adawan da su rigaya suka fito domin gudanar da wannan gangami na adawa a birnin Nairobi,wanda keda nufin gabatarwa da alummar ƙasar Raila Odinga a matsayin zaɓaɓɓen shugaban jama’a.

Ƙasar ta Kenya dai tun bayan sanar da sakamakon zaɓen na ranar 27 ga watan Disamba daya gabata,ke cigaba da kasancewa cikin ruɗani na tashe tashen hankula a sassa daban daban,bisa ga zargin magudi.

Acikin birnin na Nairobi dai,an wayi gari ayau da hargitsin mutanen da tuni suka darajawa wannan kira da jamiiyyar adawan tayi,a hannu guda kuma da ‘yansanda dake ƙokarin tarwatsa su ta hanyar harba musu barkonon tsohuwa.

Shugaban adawa Raila Odinga yace mutane bazasu amince da tauye musu haƙƙoƙi da kuma nunawa Democradiyya danniya ba.”Wannan lokaci ne na sauyi a cikin kasa,saboda kamar yadda zaa iya gani alummomin wannan kasa bazasu cigaba da buɗe idanun su, suna ganin abunda ke faruwa ba tare da ɗaukar mataki ba.Mutane bazasu cigaba da lamuntar abubuwan da gwamnatin wannan ƙasa take aiwatarwa ba.Mutane suna muradin ganin an kyautata tare da ɗaukaka Democradiyya,a maimakon matse democraɗiyya da wannan gwamnati keyi”

Gabannin sanarwar shugabannin adawan dai,ɗaruruwan magoya bayan jam’iyyar sunyi dafifi zuwa kan tituna musamman waɗanda ke garuruwan Ashanty. yunkurin Jami’an tsaro na tsaida su,ya haifar da hargitsi daya jagoranci kone konen gine gine da motoci a bangaren masu shirin gangamin dake waƙar taken Kenyan,ɗaure da fararen ƙyalle.

Hakan ne ya sanya jamian ‘yansandan suka fara harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa su.Sai dai a ta bakin jagorar wannan gangami Raila Odinga alummomin ƙasar sun gaji da halin da take ciki..”Abunda ya faru shine ,duk ƙoƙarin da alummomin wannan ƙasa sukayi na gina ƙasarsu ,wannan gwamnati ta rusa shi cikin dare ɗaya.Kuma dalili kenan daya sa jama’a ke kokarin kare martabar ta.Domin haka wannan gangami yana da matukar muhimmanci.Wannan somin taɓi ne,domin wannan batu ne da zai ɗauki lokaci mai tsawo ana gudanar dashi.

‘yan majalisar dokoki magoya bayan shugaba Mwai Kibaki dai ,sun nemi da a gurfanar da shugaban adawa Odinga a gaban kotun ƙasa da ƙasa mai hukunta masu manyan laifuffuka,adangane da abunda suka kira ruruta wutan rikicin kisan kare dangi a tsakanin alummomin Kenya.

Su kuwa yan adawan cewa sukayi umurnin da aka bawa ‘yan sanda na harbe masu wannan gangami ,shine zaa iya kwatantawa da kisan kare dangi.

Rigingimun ƙasar ta Kenya dake cigaba da gudana a kowa ne wayewanb gari dai ya tayar da hankulan shugabannin ƙasashen duniya.Ana dai cigaba da kira dangane da gano bakin zaren warware wannan rikici na siyasa daya ritsa da Kenyan dake zama zakara a ƙasashen Afrika dake martabawa Mulki irin democraɗiyya.

A hannu guda kuma ƙasashen dake makwabtaka da ita kuma suke dogaro da ita wajen man petur,sun fara shiga wani waadi na tsaka mai wuya sakamakon yankewar man dake fitowa daga Kenyan.