1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An aiwatar da hukuncin kisa akan Stanley Williams

December 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvGc

Mai bawa shugan darikar katolika na duniya shawara a fannin shari´a, wato Renato Martino yayi Allah wadai da kisan Stanley Williams da akayi ta hanyar yi masa Allurar dafi ta mutuwa.

Cadinal Renato yaci gaba da cewa kamata yayi mutane su zamo alumma masu kare rayuka amma ba wai sanadiyyar rayukan ba.

Idan dai za a iya tunawa, a tsakar ranar yau ne , jami´an gidan yarin jihar California na kasar Amurka suka aiwatar da wannan kisa ta hanyar yiwa Stanley Williams Allurar dafin.

Kotun dai data yankewa Stanley wannan hukunci tace ta same shi da laifin kisan mutane hudu a shekara ta 1979,wanda kuma kafin mutuwar tasa ya karyata.

Bugu da kari , rahotanni sun kuma tabbatar da cewa an aiwatar da wannan hukuncin ne, bayan da gwamnan jihar wato Arnold Schwarzenegger da kuma kotun kolin jihar sukayi watsi da bukatar canza wannan hukunci izuwa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.