1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An aiwatar da hukuncin kisa kan mutane 15 a Afghanistan

October 8, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8y

Kasar Afghanistan ta zartas da hukunci kisa kan wasu firsinoni 15 karon farko cikin shekaru 3. Wannan adadin shi ne mafi yawa da aka aiwatar da wannan hukuncin a kan wasu tun bayan kifar da gwamnatin Taliban a shekara ta 2001. Mutanen dai an same su da laifuka iri daban daban ciki har da kisan baki ´yan jarida da wani ma´aikacin MDD da ´yan sanda da fashi da makami da kuma yin garkuwa da mutane. A cikin wata sanarwa tawagar MDD a Afghanistan ta ce da ya fi kyau in da gwamnati ta girmama wata yarjejeniyar da aka cimma akan dakatar da hukunci kisa.