1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ba da umarnin a gurfanad da Berlusconi gaban kuliya a Italiya

July 8, 2006
https://p.dw.com/p/BurG

Wani alkali a Italiya ya umarci tsohon FM kasar Silvio Berlusconi da ya gurfana gaban kotu don fuskantar shari´a game da zargin yin zamba cikin aminci. Wannan umarnin ya biyo bayan wani binciken da aka kwashe shekaru hudu ana yi akan zargin yin almubazzaranci da dukiyar jama´a da ba da lissafi na karya game da kudadensa da kauracewa biyan haraji da kuma halatta kudin haramu a wani shirin samun izinin sayen fina-fanai ga tasharsa ta telebijin daga shekara ta 1994 zuwa 1999. Berlusconi mai shekaru 69 ya yi watsi da zargin yana mai danganta shi da wata manufa ta siyasa. Idan aka same shi da laifi, to yana fuskantar daurin shekaru 6 a gidan kurkuku. Berlusconi dai ya saba gurfana a gaban kotu kuma sau 7 yana kauracewa hukuncin dauri na zargin cin hanci da rashawa. Sau 4 ana samun shi da laifi amma ana janye hukuncin bayan ya daukaka kara.