1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bada sammacin kama kwamandan sojan Libiya

Ramatu Garba Baba MNA
August 15, 2017

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke a birnin Hague ta bayar da sammancin kama wani babban kwamandan sojin kasar Libiya da ake zargi da hannun a kisan wasu mutane 30.

https://p.dw.com/p/2iHd5
Symbolbild Internationaler Strafgerichtshof Den Haag
Hoto: Getty Images

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta ICC da ke a birnin Hague ta bayar da sammancin kama wani babban kwamandan sojin kasar Libiya da ake zargi da hannun a kisan mutane talatin da uku a birnin Benghazi. Kotun ta ICC na zargin Mahmoud Mustafa Busayf Al-Werfalli, da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama, abin da ya saba wa dokokin duniya.

Shedun da kotun ta tattara sun kunshi hotunan bidiyo da ke nuna yadda tsohon kwamandan ya galazawa wasu mutane kafin ya harbe su daya bayan daya, al'amarin ya auku ne a yayin rikicin da ya barke a kasar bayan kawo karshen gwamnatin marigayi Mamman Ghadafi a shekarar 2011.