1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bayyana yarjejeniyar Darfur a matsayin matakin farkon wanzar da zaman lafiyar a lardin

May 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuzM

Kwana guda bayan sanya hannu akan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya ga lardin Darfur mai fama da rikici dake yammacin Sudan, kasashen duniya sun bayyana haka a matsayi matakin farko na wanzar da zaman lafiya. A yau asabar an jiyo mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amirka Robert Zoellich na cewa yarjejeniyar zata bawa al´umar Darfur wata dama. Ko da yake hakan dai ba shi ne matakin karshe ba, amma shi ne mafarin samar da zaman lafiya ga lardin, sannan sai ya kara da cewa:

“Ina tsammani muhimmin abu shi ne yarjejeniyar zata ba da damar wanzar da zaman lafiya ga mutanen Darfur. Dukkan al´umomi a fadin Amirka da ma duniya baki daya sun ga yadda mutanen lardin ke zaune cikin wani mawuyacin hali a sansanonin ´yan gudun hijira. Wannan yarjejeniyar kam zata zama mafarin shirye shiryen samar da zaman lafiya a Darfur.”