1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bindige wani sojan Amirka a cikin daren jiya a birnin Bagadaza.

November 5, 2006
https://p.dw.com/p/BudO

Wani raoton da muka samu ɗazu-ɗazun nan kuma ya ce, an bindige wani sojan Amirka har lahira a birnin Bagadaza a cikin daren jiya. Kawo yanzu dai, yawan sojojin Amirkan da suka mutu a Iraqi, tun da suka afka wa ƙasar a cikin shekara ta 2003, ya tashi zuwa dubu 2 da ɗari 8 da 26, inji kamfanin diillancin labaran nan AFP, wanda ke dogaro kan alƙaluman da ma’aikatar tsaron Amirkan wato Pentagon ta buga.