1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude ofishin jakadancin Amirka a Kyuba

Gazali Abdou TasawaAugust 14, 2015

Bikin buɗe ofishin jakadancin Amirka a Kyuba na a wani mataki na maido da hulɗar diplomasiyyar ƙasashen biyu bayan zaman gaba na shekaru 54.

https://p.dw.com/p/1GFqU
Verhandlungen Cuba USA in Havana
Hoto: Reuters/Stringer

A karo na farko tun daga shekara ta 1961 an daga tutar ƙasar Amirka a ofishin jakadancin ƙasar na Kyuba. Wannan ya wakana ne a wannan Jumma'a lokacin wani biki na sake maido da huldar diplomasiyyar kasashen biyu wadanda suka yi zaman gaba na tsawon shekaru 54. Da ya ke jawabi a gurin wannan biki da ya gudana a birnin Havana Sakataren harakokin wajen Amirka John Kerry ya gargaɗi ƙasar ta Kyuba da ta rungumi tafarkin dimokraɗiyya na gaske.

" ya ce a hakikanin gaskiyya mun yi imanin cewar al'ummar Kyuba za ta fi ci gaba idan da dimokraɗiyya ta gaskiyya inda jama'a ke da hurumin zaɓen magabatanta da faɗin albarkacin bakinta da na yin addinin da ta ke so a tare da maganar tattalin arziki dama tabbatar da adalci tsakanin al'umma".

Bikin ya samu halartar jagoran juyin juyin halin ƙasar ta Kyuba Fidel Castro da sauran maƙarabansa. A watan da ya gabata ne dai aka gudanar da irin wannan biki na buɗe ofishin jakadancin ƙasar ta Kyuba da ke a birnin Washington .