1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗe taron ƙolin ƙungiyar EU a birnin Brussels

Mohammad Nasiru AwalJune 21, 2007

Taron na mayar da hankali ne wajen cimma yarjejeniya akan kundin tsarin mulkin EU.

https://p.dw.com/p/BtvI
Angela Merkel
Angela MerkelHoto: AP/LU/Toms Grīnbergs/DW

Ra´ayoyi gabanin taron sun banbanta daga masu nuna fatan cimma wani abin kirki da masu nuna shakku. Batun da ake ta da jijiyar wuya akai shi ne game da tsarin raba kuri´a a cikin KTT EU. Wannan takaddamar kuwa ta janyo wani kace-nace tsakanin Jamus da Poland. Yayin da Jamus mai shugabantar kungiyar EU ke goyon bayan aiwatar da yarjejeniya kan kundin tsarin mulki ita kuwa Poland kira ta yi da a yiwa tsarin raba kuri´ar kwaskwarima, wadda zata bawa kananan kasashe karin karfi.

Kalaman da FM Poland Jaroslaw Kaczynski yayi jim kadan gabanin bude taro sun kara rura wutar wannan takaddama. Kaczynski cewa yayi Poland zata nema a ba ta kuri´arta da aka karbe mata a lokacin yakin duniya na biyu. Ya ce inda ba´a yiwa kasarsa ta´adi a lokacin yakin ba da yanzu ta na da yawan mutane miliyan 66 maimakon miliyan 40 da take da su a yanzu. Hakika FM na son ya saka SGJ Angela Merkel cikin wani hali na kakani-kayi. To amma ta ki ta ce uffan game da wadannan kalaman.

1. O-Ton Merkel:

“Na yi imani cewa duniya ta sa mana ido yayin da al´umar Turai ke bukatar mu da mu mayar da hankali akan muhimman batutuwan da zasu suka shafe mu gaba daya. Saboda haka zamu yi iya kokarin cimma yarjejeniya a nan.”

Merkel ta kara da cewa za´a dubi bukatun kowace kasa da idanun basira ba tare da nuna bambamci ba.

Daukacin mahalarta taron na nuna damuwa game da rugujewar taron. FM Luxemburg Jean-Claude Juncker ya ce samun nasarar taron rabi da rabi ne. Wasu mahalarta taron kamar shugaban majalisar dokokin Turai Hans-Gert Pötterring sun fi nuna shakku.

3. O-Ton Pöttering:

“Take-taken na kasar Poland game da tsarin jefa kuri´a da matsayin Birtaniya game da manufofin ketare da na tsaro sun sa jiki na yayi la´asar.”

Shi dai FM Birtaniya mai barin gado Tony Blair ya ce kasarsa ka iya hawa kujerar naki a wannan fanni sannan ya nanata adawar kasarsa game da shigar da wata dokar Turai a cikin tsarin mulkin EU. Ita dai gwamnati a London na ganin yin haka tamkar yin katsalanda ne a dokokin kasa musamman wadanda suka shafi aiki da zamantakewa. Bugu da kari Birtaniya na adawa da kirkiro wani mukamin ministan harkokin wajen EU da bawa dokar EU fifiko akan dokar kasa, inji Blair.

4. O-Ton Blair:

“Mun gabatar da fannoni guda 4 wadanda muke bukatar a aiwatar da canje canje a cikinsu, kuma dole a yi wani abu a kai. A daya hannun kuma dole mu dauki kwararan matakai don inganta aikin kungiyar. Dole mu cimma wata yarjejeniya musamman yanzu da yawan kasashe a cikin EU ya ninka sau biyu.”

taron kolin dai na matsayin zakaran gwajin dafi ba ga kungiyar EU baki daya. Saboda haka kowa ya yi shirin yin tattaunawa mai tsawo.