1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗe taron ƙungiyar AU a birnin Kampala

July 25, 2010

Rikicin ƙasar Somaliya shi ne babban batu ga ƙungiyar AU

https://p.dw.com/p/OU7h
Tutar ƙungiyar AU

An buɗe taron shugabannin ƙungiyar AU a birnin Kampala na ƙasar Yuganda.Taron wanda ke samun hallartar sama da shugabannin ƙasashe 30 daga ƙasashe 53 na nahiyar, zai mayar da hankali ne akan ƙara ƙarfafa butun tsaro a ƙasar Somaliya wacce ke fama da yaƙi fiye da shekaru goma.

Sannan kuma ana sa ran shugabannin za su yanke shawara akan ƙara yawan sojoji ga rundunar tsaro ta AMISOM da ke gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a ƙasar ta Somaliya wacce kawo yanzu ta ƙumshi yawan dakaru dubu shidda na karo-karo waɗanda suka fito daga ƙasashen Ruwanda da kuma Burundi.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Halima Balaraba Abbas