1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗe taron kasa da kasa kan al´amuran tsaro a Iraƙ

March 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuQ2
FM Iraqi Nuri al-Maliki ya yi kira ga shugabannin yankin GTT da na duniya baki daya da su hada karfi da karfe don yakar ´yan ta´adda a cikin kasar sa. A lokaci daya FM ya kuma ce bai kamata a mayar da Iraqi tamkar filin daga na wasu kasashe da ba sa ga maciji da juna ba. Maliki ya bayyana haka ne a jawabin bude wani babban taro yini daya a birnin Bagadaza da nufin samun taimako don kawo karshen tashe tashe hankula a Iraqi. Kasashe 6 makwabtan Iraqi da membobin dindindin na kwamitin sulhun MDD da wakilan kasashen Larabawa da dama na halartar taron. An yi ta yada jita-jita ko Amirka zata tattauna kai tsaye da Iran da kuma Syria a gefen taron. Jami´an Amirka sun ce ba zasu kau da kai su yi tafiyar su ba, idan wakilan Iran da na Syria suka tuntube su. Kakakin gwamnatin Iraqi ya ce wakilan Amirka, Iran da kuma na Syria sun yi musafaha a zauren taron.