1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗe taron sasanta al´umar Somalia a Mogadishu

July 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuGI

A cikin tsauraran matakan tsaro an fara babban taron sasanta al´umar Somalia a Mogadishu babban birnin kasar. To sai dai masu kishin Islama sun yi barazanar katse taron. Wakilai fiye da dubu daya na kabilu da tsofafin madugan yaki da kuma ´yan siyasa ke halartar taron. Kakakin gwamnatin rikon kwaryar Somalia Abdi Haji Gobdon ya ce an dauki dukkan matakan da suka wajaba don samun nasarar wannan taro wanda ke a matsayin wata dama ta karshe ga shugaban wucin gadi Abdullahi Yusuf na samar da zaman lafiya mai dorewa a Somalia.

Gobdon:

“A da mun fuskanci rigingimu, amma yanzu kurar rikici ta lafa. Mun kammala dukkan shirye shirye da suka kamata. Jami´an tsaro ne ke iko da ko-ina. Kuma taron zai tafi salim alim.”

A karshen shekara ta 2006 dakarun Ethiopia suka taimaka aka fatattaki sojojin sa kai na kotunan Islama daga birnin Mogadishu, to sai dai har yanzu ana ci-gaba da dauki ba dadi a babban birnin na Somalia.