1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude babban taron kasashen Afirka a Bonn

November 5, 2005
https://p.dw.com/p/BvMQ

Shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler ya bude wani babban taro shugabannin Afirka a nan birnin Bonn don duba sabbin hanyoyin taimakawa nahiyar. Taron na yini biyu wani sabon shirin ne da shugaban na Jamus ya gabatar da nufin kulla kawance da nahiyar Afirka, wanda zai bude wata sabuwar kofar yin shawarwari tsakanin kasashe masu arzikin masana´antu da takwarorinsu na Afirka. Mahalarta taron a Pertersberg dake nan Bonn sun hada da ´yan siyasa da manyan ´yan kasuwa da masana da ´yan jaridu daga Turai da Afirka kuma zasu tattauna akan yadda Afirka zata inganta kanta da kanta tare da hanyoyin da za´a bi wajen inganta manufofin taimakon raya kasashe masu tasowa. Shugaban ATK Thabo Mbeki da shugaban Olusegun Obasanjo na Nijeriya na daga cikin shugabannin Afirka dake halartar taron.