1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN BUDE TARON KASA DA KASA DON SHAWO KAN YADUWAR TA'ADDANCI A DUNIYA - A BIRNIN MADRID.

Yahaya AhmedMarch 10, 2005

A taron da aka bude a birnin Madrid (9. ga watan Maris) na kasar Spain, don tatauna batun matsalar yaduwar ta'addnci a duniya, mahalarta na kokari ne wajen samo hanyoyin tinkarar wannan bala'in a fagen siyasar kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/Bvco
Harin bam da aka kai kan jirgin kasa a birnin Madrid a cikin watan Maris na shekara ta 2004.
Harin bam da aka kai kan jirgin kasa a birnin Madrid a cikin watan Maris na shekara ta 2004.Hoto: AP

Mahalarta taron na birnin Madrid, sun yarje kan cewar, matakin da ya fi kyau a dauka wajen tinkarar batun yaduwar ta’addanci shi ne rigakafi. Ba kawai gano alamun gudanad da wadannan munanan ayyukan ne, zai hana aukuwarsu ba. Kamata ya yi a bi diddigin dalilan da ke tunzura mutane su rungumi wannan akidar tun da farko. Ta hakan ne za a iya magance matsalar, tun ba ta sami saiwa ta kankama ba. Ban da hakan kuma, kwamiti daban-daban na taron da aka kafa, na nazari ne wajen tabbatad da ummal’aba’isin wannan annobar a huskar siyasa da kuma fannin ilimin halayyyar dan Adam, ko kuma Psychology a turance.

Amma wasu masana a fannin siyasa, kamar Luise Richardson ta jami’ar Harvard ta Amirka, na kira ne ga yin taka tsantsan wajen tsai da shawar cikin gaggawa, ba tare da duban lamarin da idon basira ba. Kamar dai yadda ta bayyanar:-

"Talauci ba shi ne dalilin da ke janyo ta’addanci ba. Sauyin da ake ta samu cikin gaggawa a fannin tattalin arziki da kuma salon nan na hadayyar tattalin arziki ko kuma "globalisation", su ne abin da za a iya kira kasadar da ke renon akidar ta’addanci."

Jama’a da dama dai na huskantar wadannan canje-canjen halayyar tattalin arziki ne tare da tsoro da kuma takaici. Hakan kuma ke janyo matukar bacin ransu, har ya kai ga neman mafita, inda a galibi suke fadawa hannun masu yada wannan akidar ta ta’addanci.

A nan dai, masana fannin ilimin halayyar dan Adam na da muhimmiyar rawar gani da za su iya takawa. Har ila yau, wani abin gaibu ne ga masana wannan fannin, yadda mutum daya mai bin wannan akidar, ke iya shawo kann dimbin yawan jama’a su biye masa ba tare ma da sun yi tunani kann abin da suke yi ba. To a bangaren masana fannoni daban-daban ke nan.

A fannin siyasa kuwa, kungiyoyin kare hakkin dan Adam da suka halarci taron, sun yi kakkausar suka ne ga manufofin da shugaba Bush na Amirka ya sanya a gaba. Kenneth Roth, babban darektan kungiyar nan Human Rights Watch ta Amirka ya zargi Bush ne da cewa, yana ta jawabai kann `yanci, da dimukradiyya da samun walawalar jama’a, amma ko sau daya bai taba takalo batun hakkin dan Adam ba. Hakan kuwa alamar munafunci ne, wadda kuma ke dusashe kwarjinin Amirkan a idon duniya baki daya. Roth dai ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ta mai da himma wajen tabbatar da adalci a duniya. Ta hakan ne za a iya shawo kan duk masu niyyar rungumar akidar ta’addanci su yi watsi da ita, tun ma ba su dandana abin da take kushe da shi ba.

A yau ne dai ake sa ran babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan, zai wa taron jawabi. An dau tsauraran matakan tsaro a babban birnin na Spain, don kare lafiyar manyan bakin da ke halartar taron, wadanda suka hada da sarki Juan Carlos na Spain , da babban sakataren Kungiyar NATO, Jaap de Hop Scheffer, da shugaban Hukumar kungiyar Hadin Kan Turai, Jose Manuel Barrosso. Kazalika kuma shugabannin kasashen Afghanistan, da Aljeriya, da Jumhuriyar Dominican da Pakistan da Portugal na halartar taron.