1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude taron shugabannin kasashen yan baruwammu a Havana

Zainab A MohammadSeptember 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bty8

A yau ne aka bude taron kungiyar kasashen yan ba ruwammu a birnin Havana,kasar Cuba wanda ke samun halartan kimanin shugabannin kasashe 55.

An bude taron kasashen yan baruwammu din ne a karkashin jagorancin mukaddashin shugaban kasar Cuba Raul Castro,wanda ke kann wannan matsayi tun daga karshen watan yuli,sakamakon jinya da dan uwansa fidel Castro yakeyi daga tiyata da akayi masa.

Sakatare general na mdd Kofi Annan wanda tun a jiya ya isa birnin Havana domin halartan taron kasashen ya ba ruwammun,ya gana da shugaba Fidel Castro a gadon jinyarsa a asibiti.

Ayayin wannan ganawarsu dai shugaban Cuban da jagoran mdd sun yi musayan raayoyinsu adangane da muhimmancin wannan taro da kuma wasu batutuwa da suka shafi kasashen duniya da suka hadar da rigingimun yankin gabas ta tsakiya ,da halin da nahiyar Afrika ke ciki.

Mukaddashin shugaban Cuba kuma ministan tsaron kasar,Raul Castro ya marabci manyan shugabannin kasashe dake halartan wannan taron da suika hadar da mahmud Ahmadinejd na Iran, da Hugo Chavez na Venezuala da shugaba Gloria Arroyo da prime minista Portia Simpson-Miller na jamaica.

Kungiyar kasashen yan baruwammun dai na daya daga cikin kungiyoyi da suka marawa Iran baya adangane da rikicin Nuclear datake fama dashi.

Shugaban Belarus,kasar Amurka ta bayyana da kasancewa inda ake mulkin kama karya,wadda ta nemi hadin wakilan kasashen 11 dake kungiyar,Alexander lukashenko,shima na halartan taron na kasar Cuba.

Shugaba Ahmadinejad na Iran na halartan wannan taro ne adaidai lokacin da Amurka ke dada matsa kaimi dangane da kakabawa tehran takunkumi ,saboda watsi datayi da waadin 31 ga watan augustan daya gabata ,dangane da dakatar da bunkasa sinadran uranium dinta.

Shugaban na Iran dai ya samu goyon baya daga shugaba Chavez na Venezuela,a wajen taron kasashe 18 masu tasowa,wanda aka bude jiya a birnin na havana.

A taron da suka bude a yau dai anasaran shugabannin kasashen yan baruwammu zasu cimma yarjejeniya guda,wadda zata jaddada cewa Iran na ikon amfani da harkokin nucleanrta domin samar da wutan lantarki da wasu bukatu nata.

Bugu da kari anasaran kasashe masu makaman nuclear kamar India da Pakistan,suma zasu taka muhimmiyar rawa a taron shugabannin kungiyar da zai gudana zuwa gobe asabar.

Sakatare general na mdd Kofi Annan zaiyi jawabi wa mahalarta wannan taro,wanda aka bude ayaui bayan taron sharan fage da aka dauki kwanaki 4 ana gudanarwa.

Bugu da kari taron zai tattauna matsalolin taaddanci da yadda zaa kalubalance shi a duniya baki daya.