1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci ICC ta binciki rikicin Siriya

Abdul-raheem Hassan
October 11, 2016

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya jaddada bukatar kotun hukunta laifukan yaki ta gudanar da bincike kan rikicin Siriya.

https://p.dw.com/p/2R5tY
UN-Generalsekretär Ban Ki-moon
Hoto: Picture-Alliance/M. Girardin/Keystone

Ban Ki-moon ya gabatar da wadnnan bukatu ne a lokacin da yake bayyana kaduwarsa a kan mawuyacin halin da mazauna birnin Aleppo ke ciki. Ban ya kuma nuna takaici kan yadda kwamitin tsaron ya gaza cimma matakan da suka dace a zaman da ya gudanar a karshen mako. Babban sakataren ya ce duk da cewa yunkurin gabatar da irin wannan bukata ya fuskanci cikas daga kasashen Rasha da Sin a shekara ta 2014, to amma ya jaddada kudirinsa na ganin sake mika koken ga kotun hukunta manyan laifukan yaki. Kotun ta ICC zai taka muhimmiyar rawa na kawo karshen rikicin da ya hallaka sama da mutane 2,8000 cikin shekaru biyar a kasar Siriya.