1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci karin tallafi ga yankin Darfur dake Sudan

March 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5D

Shugaban hukumar bayar da tallafi na Mdd, Jan Egeland, ya bukaci kasashe masu hannu da shuni dasu rubanya irin tallafin da suke bayarwa a yankin Darfur dake Sudan.

Bukatar hakan a cewar babban jami´in, yazo ne bisaa la´akari da irin matsanancin hali na rayuwa da dubbannin mutane a yankin ke ciki.

Mr Egeland, wanda aka shirya cewa nan da yan makonni kadan zai kai wata ziyarar aiki izuwa kasar ta Sudan da Chad da kuma Uganda, ya tabbatar da cewa a yanzu haka akwai mutane miliyan 3 da digo uku dake cikin kunci na rayuwa a yammaci da kudancin kasar ta Sudan.

Bugu da kari jami´in na Mdd ya kuma bukaci gaggauta daukar matakan kawo karshen irin balahirar dake wakana a yankin na Darfur, ta hanyar cimma sulhu a tsakanin bangarorin dake rikici da juna.