1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An Bukaci yankewa Sadam Hukuncin kisa

Zainab A MohammedJune 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6b

A yau ne aka koma zaman shariar tsohon shugaban Iraki Sadam Hussein da mukarrabansa guda 7 a birnin bagadaza,inda tawagar masu shigar da kara suka bukaci a yankewa wadanda ake karan hukuncin kisa.A jawabinsa na karshe a dangane da wannan kara,babban lauya mai shigar da kara ,yace Sadam da na hannun damansa sunyi amfani da batun yunkurin hari akan ayarin motocin shugaban kasa a shekarata 1982,a matsayin dama na kaddamar da hari wa yan shia dake kauyen Dujail.Jagoran masu shigar da karan ya fadawa kotun cewa asakamakon hakane aka azabtar da shiawan wadda takaisu ga mutuwa,kana wasu kuwa akayiwa kisan gilla.Bayan yunkurin hari wa ayarin motocinsa ne,Sadam yabada umurnin hari wa kauyen Dujail.