An cafke masu ayyukan ta´addanci a Biritaniya
January 31, 2007Yan sanda a Biritaniya sun cafke wasu mutane takwas da suke zargi na da alaka da ayyukan ta´addanci.
Hakan kuwa ya faru ne a wani mamaye na ba zata da jami´an yan sandan suka kai izuwa birnin Birmingham.
Rahotanni dai sun rawaito cewa mutane takwas din da aka cafken na da alaka ne da kasashen Biritaniya da kuma Pakistan
A cewar yan sanda masu bincike, an kame mutanen takwas ne, bisa zargi da ake musu na kokarin shiryawa tare da aiwatar da ayyukan ta´addanci a kasar ta Biritaniya.
Duk da cewa aiwatar da wannan aiki bai samu cimma nasara ba, kafafen yada labarai na Biritaniya sun shaidar da cewa, an so a aiwatar da ayyukan ta´addancin ne ta salo na yin garkuwa da mutane.
Idan dai an iya tunawa, ko da a makon daya gabata, sai da jami´an tsaron na Biritaniya suka kai irin wannan hari a arewacin kasar.