1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cafke mataimakin kungiyar Boko Haram a Najeriya

April 3, 2016

Rahotanin da ke futowa daga tarayyar Najeriya na nuni da cewar rundunar sojojin kasar ta cafke jagoran kungiyar masu jihadi ta Ansaru Khalid al-Barnawi da ke zama mataimakin kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1IOoY
Nigeria Armee Task Force gegen Islamisten Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP

Kazalika Khalid al-Barnawi wanda kuma ke zama daya daga cikin mutane uku da mahukuntan Amirka suka zayyana sunayen su a shekara ta 2012 a matsayin futattun 'yan ta'adda.

Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Brigediya Janar Rabe Abubakar shi ne ya bayyana hakan, a inda ya kara da cewar jami'an tsaron sun sami nasarar cafke shi ne a ranar juma'ar nan a garin Lokoja da ke cikin jihar Kogi a Arewacin Najeriya.

Shi dai Kahalid al-Barnawi da ke zama mataimakin Shugaban kungiyar Boko Haram na daya daka cikin futattun jerin mutanen da rundunar sojojin Najeriya take nema ruwa a jallo a yakin da suke na kakkabe masu ayyukan kungiyar Boko Haram.

Cafke jagoran Ansarun ya sake karfafawa jami'an Najeriyar kwarin gwiwa a yakin da suke da kungiyar Boko Haram wanda hakan ke zama nasarar baya bayan nan da rundunar sojojin ke cigaba da samu a duk fadin kasar.