1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cafke mutane sama da 300 a Gaɓar Yamma da Ƙogin Jordan.

September 1, 2010

Dakarun tsaron Falisɗinawa sun kame waɗanda ke da alaƙa da mayaƙan ƙungiyar Hamas.

https://p.dw.com/p/P24e
Alama ta ƙungiyar HamasHoto: AP

Dakarun tsaron Falasɗinawa sun cafke sama da wasu mutane 300 da ke da alaƙa da ƙungiyar Hamas a yankin Gaɓar Yamma ta Ƙogin Jordan. Shi dai wannan kame an yi shi ne bayan da sashin masu ɗauke da makamai na ƙungiyar suka harbe wasu Yahudawa 'yan - kama wuri zauna guda huɗu a daf da garin Hebron. A yammacin ranar Talata ne Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton ta yi Allah wadai da wannan hari a bayan da ta kammala tattaunawa da firaministan Israila, Benjamin Natanyahu. A cewar ƙasar ta Amirka dai wannan kisan ba zai yi ƙafar ungulu ga shirin zaman lafiyar da ake yunƙurin ƙullawa ba. Haka nan shi ma shugaban Falasɗinawa, Mahmoud Abbas da Firaminista Salam Fayyad sun yi Allah wadai da wannan hari da aka kai wa fararen hula.

A ranar Alhamis ne idan Allah ya yarda, shugabannin biyu za su buɗe wata tattaunawa da Shugaba Barack Hussein Obama a fadar White House. Ƙungiyar ta Hamas dai ba a sanya ta cikin tattaunawar kai tsaye ba, a watanni 18 ɗin da suka gabata. Tuni dai Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi na'am da taron samar da zaman lafiyar. Babban fatan Kantomar kula da harkokin ƙetare a ƙungiyar, Catherin Ashton, shi ne warware taƙaddamar: Ta ce "Munyi amannar cewar, kamata ya yi tattaunawa ta kai ga cimma daidaiton samar da 'yantacciyar ƙasar Falasɗinu, mai bin tafarkin dimuƙraɗiyya, wadda kuma za ta zauna daura da Isra'ila da kuma sauran waɗanda ke makwabtaka da ita cikin zaman lafiya da lumana."

Mawalafi: Saleh Umar Sani

Edita: Halima Balaraba Abbas