1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cafke wasu mutane biyu da ake tuhumarsu da kasancewa 'yan Al-Ka'ida

January 24, 2005

A jiya lahadi da sanyin safiya mahukuntan Jamus suka kame wasu Larabawa guda biyu bisa tuhumarsu da kasancewa 'ya'yan kungiyar Al-Ka'ida

https://p.dw.com/p/BvdX

Kimanin jami’an ‚yan sanda 65 suka yi wa gidajen Ibrahim Muhammed da Abu Yasser a biranen Mainz da Bonn kofar rago da sanyin safiyar jiya lahadi, inda suka binciki dakunansu domin tara bayanai na shaidar laifukansu sannan aka tasa keyarsu zuwa gidan wakafi. Ana dai zarginsu da kasancewa ‚ya’yan wata kungiyar ta’adda ta ketare. Ana tuhumar dukansu biyu da kasancewa ‚ya’yan kungiyar Al-Ka’ida. An ce suna da dangantaka ta kut-da-kut da Ramzi Binashibi, wanda ake zarginsa da hannu dumu-dumu a hare-haren ta’addancin nan na sha daya ga watan satumban shekara ta 2001. Ibrahim Muhamme dake rike da takardar fasfo ta Jamus, kamar yadda bayanai suka nunar, ya sha neman horo a sansanin ba da horo na kungiyar Al-Ka’ida a kasar Afghanistan da kuma saduwa da Osama Bin Ladin kai tsaye. An dai saurara daga babban mai daukaka kara da sunan gwamnati a nan Jamus Kay Nehm yana mai bayanin cewar:

Shuagabannin Al-Ka’ida ne suka dakatar da shi daga niyyarsa ta farko a game da shiga rukunin masu kai harin kunar bakin wake domin mutuwar shahada. A maimakon haka aka danka masa wani alhakin na tafiyar da jihadi a sassa dabam-dabam na duniya. Kuma a saboda kasancewar yana rike ne da takardar fasfo ta Jamus da kuma ikon kai da komo a tzsakanin kasashen KTT, sai aka dora masa alhakin nemo sabbin membobi da kuma wasu ‚yan sa kai da zasu rika kai hare-haren kunar bakin wake.

A cikin watan satumban da ya gabata ya samu kafar shawo kan Abu Yasser a garin Mainz. Da farko, shi Abu Yasser yayi inshora ta ko ta baci akan tsabar kudi Euro dubu 800 tare da niyyar haddasa wani mummunan hadarin mota a kasar Masar. Bayan ikirarin mutuwarsa sai danginsa su dauki lauya, wanda zai taimaka musu karbar wadannan kudade a nan Jamus. Sannan shi kuma ya zarce zuwa Iraki yana mai jiran umarnin kai harin kunar bakin wake.

Bisa ta bakin babban mai daukaka karar da sunan gwamnati Kay Nehm, Ibrahim Muhammed yayi bakin kokarinsa wajen sayen wasu kayayyakin nukiliya a kasar Luxemburg, amma daga baya an dakatar da wannan shiri. A yau litinin ne ake gabatar da su gaban mai shari’a domin yanke kuduri a game da ba da umarnin tsaresu a gidan wakafi.