1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto yan kasar Sin wadanda akayi garkuwa dasu a Naija Delta

January 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuUD

Jamian kasar Chine sun sanarda ceto yan kasar su 5 wadanda akayi garkuwa da su a yankin naija Delta makonni biyu da suka shige.

Maaikatar harkokin cikin gida ta China tace yau laraba aka sako wadannan mutane kuma suna cikin koshin lafixa.

Tsageran yankin Naija Delta suka sace maaikatan harkokin sadarwar ta China su biyar a farkon wannan wata.