1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cika shekara guda da mutuwar Raffik El Hariri

February 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv86

A birnin Beruth na kasar Labanon, a kalla mutane dubu dari 5 ne, su ka hallarra a wani gagaramin taro, domin tuni da shekara guda daidai, da wasu yan takife, su ka hallaka tsofan Praminista Raffik Alhariri.

Wannan kissan gilla, ya haifar da juyin juya hali, a fagen siyasar kasar Labanon.

A sakamakon sa, Syria ta janye dakararun ta, dake kasar, bayan shekaru 30, sannan ann shirya zabuka bisa tsantsar demokradiya.

Albarkacin ranar ta yau, hukumomin kasar Labanon, sun baza jami´an tsaro cikin shirin ko ta kwan.

Jagororin wannan zanga zangar luma sun gabatar da bayyanai, inda su ka ci gaba, da kalubalantar katsa landar, da kasar Syria ke yi, ga harakokin cikin gida na Labanon.

A daidai karfe 12 da minti 55, agogon Labanon, wato karfe 10, da miniti 55 ,agogon GMT dubunan mutanen su ka yi tsit, na tsawan mintin guda, domin a daidai wannan laokaci ne a sheakara da ta gabata a ka aikata kissan Raffiik Alhariri.

A yayin da ya ke jawabi gaban jama´a, dan mirganyin, wato Sa´ad Hariri, da a halin yanzu, ya shiga harakokin siyasa,ya yi godiya ga al´umar kasar Labanon, ya kuma kire su, zuwa hadin kai.

Bugu da kari ,Sa´ad Hariri, ya bukaci a gudanar da addu´´o´i, ga dukan mutanen da su ka kwanta dama, a sanadiyar ra´ayoyin su, na kwato Labanon daga tutar kasar Syiria.