1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cika shekaru 50 da ƙaddamar da juyin juya hali a Hongrie

October 22, 2006
https://p.dw.com/p/Buev

A yau ne a ka fara bikin cikwan shekaru 50 daidai, da al´ummomin Hongrie, su ka tada bore, domin kwatar yanci daga mulkin danniyar da Russia ta yi masu.

Albarkacin wannan rana, shugaban ƙasar Hongrie,, Laszlo Solyom, ya gabatar da jawabi gaban duɓin jama´ar ƙasa, da kuma tawagogi daban- daban daga ƙetare.

A ƙalla shugabanin ƙasashe 18, daga nahiyar turai, da su ka haɗa da Höst Khöler, na Jamus su ka halarci wannan gagaramin biki.

Kamar dai yada tarihi ya nunar, ranar 23 ga watan oktober na shekara ta 1956 ne, dubunan jama´a, a birnin Budapest su ka shirya zanga-zangar ƙin jinin mulkin communisanci, da Russie ta ƙaddamar a ƙasar.

Duk da kashe kashen kan mai uwa da wabi, da dakarun Russie su ka yi wa masu zanga-zangar, al´ummar Hongrie ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, har lokacin da ta cimma buri, kussan shekaru 20 da su ka gabata.