1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cika shekaru 50 da kafa dokar shiga aikin soji don bauta wa ƙasa a Jamus

Yahaya AhmedJuly 7, 2006

Tun shekaru 50 da suka wuce ne aka kafa dokar shiga aikin soji na bauta wa ƙasa a nan Jamus, dokar da ke tilasa wa duk wani matashi mai shekaru 18 da haihuwa, ko kuma sama da haka, yin aikin soji na tsawon watanni 18.

https://p.dw.com/p/BtzM
Wani kurtun rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr
Wani kurtun rundunar sojin Jamus ta BundeswehrHoto: dpa - Bildarchiv

Tun ran 7 ga watan Yulin 1956 ne aka kafa dokar shiga aikin soji na bauta wa ƙasa a nan Jamus. Bisa wannan dokar, tilas ne ga duk wani matashi mai shekaru 18 da haihuwa, kuma mai cikakken lafiya, ya yi aikin soji na bauta wa ƙasa, har tsawon watanni 18. Wannan dokar dai tana ci har yanzu, duk da kiran da ɓangarori da dama ke yi na a soke ta, saboda manufar kafa ta, ta dusashe tun kawo ƙarshen yaƙin cacar baka.

A daidai lokacin cika shekaru 50 da kafa dokar, wasu matasa sun fara aikinsu na bauta wa ƙasa tamkar kurata, a rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr.

Waɗannan kuratan sun fara aikinsu ne a wata bataliyan rundunar Budeswehr ɗin da ke Brandenburg kusa da birnin Berlin. Ɗaya daga cikinsu ya bayyana irin yadda ya ji, a farkon ranakun da ya fara aikin soji:-

„Da farko dai babu abin da muka yi daidai. Amma kowa ma da haka yake farawa. Dukkanmu, ba mu san juna ba kafin mu iso nan. Kuma sai ga shi, oda ake ta ba mu, ta yadda za mu tafiyad da komai a nan barikin. Da farko ko maci ma ba mu iya yi sosai ba, kowa na tsayawa ne yadda ya ga ya dace masa.“

Tun da aka kammala yaƙin duniya na biyu kawo yanzu dai, kusan Jamusawa miliyan 8 ne suka yi aikin soji na bauta wa ƙasa, a rundunonin mayaƙan sama da na mayaƙan ruwa da kuma sojojin igwa. A halin yanzu dai, an rage tsawon lokacin aikin sojin zuwa watanni 9 kawai. Amma duk da haka, kusan kashi 20 cikin ɗari kacal na matasan ne kawai ke kai kansu shiga aikin bauta wa ƙasar a rundunar sojin ta Bundeswehr. Ko mene ne dalilin haka? Wani mai horad da matasa aikin soji a barikin Brandenburg ya bayyana cewa:-

„Irin halin rayuwar kurtun soja a bariki, inda mutane huɗu ke zaune a ɗaki ɗaya, mai murraba’in mita 18 zuwa 20, ga gadajensu kuma, irin tagwayen nan da ake ɗora ɗaya bisa ɗaya, wato duk a ganin matasan, wani matsin lamba ne gare su.“

Wanda bai yi aikin sojin ba dai, to dole ne ya yi wani aiki daban na bauta wa ƙasa. Sai dai, saboda dalilan rashin lafiya, ba zai iya yin aikin ba. Malaman horad da matasa aikin sojin dai na ta ƙara nuna damuwarsu ga koma bayan yawan matasan da ake samu a ko wace shekara. Ƙararrakin da ake ta ɗauka a kotu kuma game da dai shiga aikin sojin a kan dole, wato suna kasancewa wata barazana ga makomar shirin ma gaba ɗaya, inji malaman. Shirin dai, bai sami farin jini ba, tun da aka ƙiƙiro shi a shekaru 50 da suka wuce. Tun wannan lokacin ne ake ta ƙorafi a kansa a majalisa. Kafin ma a zartad da dokar, a ran 7 ga watan Yulin 1956, sai da aka yi wata muhawara mai tsanani har tsawon sa’o’i 20, a majalisar dokoki ta Bundestag. A wannan lokacin dai, ’yan jam’iyyar Social Democrats, wato SPD ne riƙaƙƙun masu adawa da shirin. To sai ga shi kuma yau, su ne ma ke neman a ci gaba da shi. Ɗaya daga cikin magoya bayan shirin a halin yanzu dai, shi ne tsohon ministan tsaro na tarayya Peter Struck, daga jam’iyyar ta SPD. Kamar yadda ya bayyanar:-

„A yau dai, akwai mutane da dama da ke sha’awar sanin duk abin da ke wakana a rundunar Bundeswehr, saboda ko wannensu na da ɗa ko kuma wani daga cikin iyalinsu da ke aiki a rundunar. A nawa ganin dai, idan aka maye gurbin wannan rundunar da masu aikin soji tamkar sana’a, to za a sami taɓarɓarewar wannan hulɗar da jama’a. Kuma na san cewa, duk wata hulɗa da aka yi da sojoji na sana’a, ba abin faranta rai ba ne.“

Ba dai tsohon ministan kaɗai ne ke nuna goyon bayan shirin shiga aikin soji na bauta wa ƙasar ba. Shugaban ƙasa na yanzu, Horst Köhler ma na goyon bayan wannan shirin. Shugabannin siyasa da dama dai na ganin rundunar Bundeswehr ɗin, tamkar wata kafa ce ta ƙarfafa tafarkin dimukraɗiyya a nan ƙasar a halin yanzu. Amma a lokacin da aka ƙaddamad da shirin, wato ana hangen iya ɗaukan matakan mai da martani ne ga duk wani harin da rukunin tarayyar Soviyet da ’yan kurarta za su iya kawo wa Jamus da ƙasashen Yamma.

A yau kuwa, bayan kawo ƙarshen yaƙin cacar baka, masu tsara shirye-shiryen tsaro na ganin cewa, ba yawan dakaru ake bukata ba kuma kamar a da. Ƙwararrun rukunai ake bukata, waɗanda kuma cikin gaggawa, za a iya tura su zuwa ko’ina a duniya inda mummunan rikici ya ɓarke, don yin katsalandan da kuma kwantad da tarzoma. A ƙasashe da dama na Ƙungiyar Haɗin Kan Turai dai, tuni an soke shirin aikin sojin na bauta wa ƙasa.