1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma matsaya a yaki da dumamar yanayi

Yusuf BalaDecember 12, 2015

Kasashen duniya na kallon yarjejeniyar a matsayin wacce ta kafa tarihi, inda sassa da suka halarci taron na Paris suka amince da kashe Dala dubu 100 saboda sauyin na yanayi.

https://p.dw.com/p/1HMKA
Frankreich Cop21 Klimagipfel in Paris
Shugaba Holland da Fabius da Ban Ki moonHoto: Reuters/S. Mahe

Mahukunta a kasar Faransa suka ce kasashe 195 sun yi dakon ganin lokacin cimma sabuwar yarjejeniyar rage kaifin tasirin dumamar yanayi a duniya. A lokacin da ya ke jawabi a yayin taron cikin kalamai masu susa rai, ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya ce numfashin duniya ta tsaya cak don ta ji irin matsayar da muka cimma, dan haka mun cimma aniya ta rage dumamar da duniya ke yi da digiri biyu idan aka samu dama mu rage da kashi daya da rabi.

Ya ce za a samar da kudi Dala miliyan dubu 100 a shekara tun daga shekarar 2020 don tallafawa kasashe masu tasowa su rage radadin da suke fuskanta saboda sauyin na yanayi. Fabius ya ce wannan daftari da ya zama dole a tabo kowane fanni a cikinsa ya kunshi duk wata bukata kan wannan sauyin yanayi wanda ba a yi ba a baya, ya kuma bi sharuda ne da aka cimma a Durban a shekarar 2011.

Da yake tsokaci kan wannan yarjejeniya da aka cimma Ban ki-mMoon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya zama wajibi ga wakilan taron su tabbatar da ganin an aiwatar da abubuwan da aka cimma a aikace. Shi ma Shugaba Hollande na Faransa ya ce kasashen duniya sun rungumi wannan matsaya.