1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma yarjejeniya tsakanin kabilun Mogadishu da dakarun Habasha

Hauwa Abubakar AjejeMarch 23, 2007

Rundunar sojin kasar Habasha ta cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninta da shugabanin kabilar Hawiye domin kawo karshen tashe tashen hankula a babban birnin kasar Mogadishu

https://p.dw.com/p/Btvx
Hoto: AP

Wannan yarjejeniya dai ta zo kwana guda bayan gwamnatin wucin gadi ta Somalia ta lashi takobin ci gaba da fada har sai ta ci nasara akan sojin sa kai na kungiyoyin islama a kasar,wadanda mafi yawansu suka fito daga kabilar ta Hawiye dake birnin Mogadishu,wadanda kuma ske zargi da kai hare hare a birnin.

Kakakin dattijan kabilar ta Hawiye Ugas abdi Dahir Muhammad yace bayan muhimmiyar tattaunawa kan halin siyasar kasar da kuma sabon fada daya barke,sun amincr tsakanisu da sojojin Habasha dasu kaddamar da wannan yarjejeniya ta tsagaita bude wuta.

Yace sojojin na Habasha zasu kasance a sansanoninsu na soji kuma ba zasuyi fada day an kasar Somalia ba,su kuma a nasu bangare yan kabilar Hawiye ba zasu harba koda harsashi daya ba kuma zasu mutunta wannan yarjejeniya.

Muhammad yace yarjejeniyar ta kuma shafi dakarun Somalia wadanda suka dogara akan takawarorinsu na Habasha wadanda suka fi su samun horo da kayan aiki.

Wakilin kanfanin dillancin labaru na AFP yace birnin Mogadishu a safiyar jumaan nan akwai dan kwanciyar hankali bayan kwanaki biyu a jere na harbe harbe da sukayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 24 darururwa kuma suka samu raunuka.

Sai dai kuma mazauna birnin sunce yawan wadanda suka rasa rayukansu zasu fi haka tunda a cewarsu baa iya kaiwa ga wuraren da fadan yafi kamari.

Jamian rundunar sojin Habasha sun tabbatar wannan ganawa tsakanin yan Kabilar Hawiye a gidan madugun yaki Abdi hassan Awale Qeybdid a Mogasdishu,sai dai basu ce komai ba game da yarjejeniyar.

Majiyoyi daga kabilar ta Hawiye kuma sunce wannan yarjejeniya itace ta farko tun bayanda sojojin Somalia tare da taimakon dakarun Habasha suka kori mayakan islama daga kudanci da kuma tsakiyar Somalia a watan janairu wanda kuma ya haddasa yakin sunkutru da yayi sanadiyar rayukan mutane da dama.

Somalia kasa dake da jamaa kusan miliyan 10,tana cikin tashin hankali tun 1991 lokacinda aka hambarar da gwamnatin Muhammad Siad Barre wanda ya janyo gwagwarmaya na neman kafa iko a kasar.