1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma yarjejeniyar sako dan kasar Jamus da iyalensa a Yemen

December 30, 2005
https://p.dw.com/p/BvER

Wani babban mai shiga tsakani a sace bajamushen nan da iyalansa yace,an cimma yarjejeniya sako tsohon mataimakin ministan harkokin wajen na Jamus da iyalansa,da wasu yan kabila suka sace suna masu neman a sako yan uwansu da suke daure.

Sheikh Awadh Bin al-Wazir,memba na majalisar Yemen kuma babban mai shiga tsakani,yace kabilun sun amince su sako mutanen da suka garkuwan da su kafin safiyar gobe asabar idan har masu shiga tsakanin sun maye gurbin mutanen.

Al-Wazir yace, sun amince da bukatun yan kabilar bayan tattaunawa da shugaban kasar Yemen da wasu jamiansa.

Jürgen Chrobog dan shekaru 65,ya riki matasyin mataimakin minista karkashin mulkin Gerhard Schroeder,ya kuma taba zama jakadan Jamus a Amurka.