1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin KOrea ra Kudu da ta Arewa

October 4, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9R

A sakamakon taron ƙolli na kwanaki 3 da su ka shirya, shugabanin ƙasashen Korea ta Arewa da ta kudu da ke maƙwbaka da juna, sun cimma matsaya ɗaya ta shifiɗa zaman lahia tsakanin su.

Shugaba Kim Il Song, na Korea ta Arewa da takwaran sa Roh Moo-Hyu na Korea ta Kudu sun alkawarta aiki kafaɗa da kafaɗa, domin samar da zaman lahia mai ɗorewa tsakanin ƙasashen 2, wanda ke zaman gaba tun shekara ta 1953, a sakamakon yaƙin cacar baka na manyan ƙasashen dunia.

Kazalika sun alƙwarta fara da tantanawa a wata mai zuwa, tare da Amurika da Sin, wanda ke da ƙarfin fada aji, a ƙasashen da zumar cimma wannan buri.

Saidai masu kula da harakokin diploamtia da na siyasa a wannan yanki, na hasashen cewar, wannan yarjejinya, ba zata cimma abun azo a gani ba, ta fannin ɗinke ɓaraka tsakanin wannan ƙasashe.