An dakatar da wasu alƙalai a Ghana
September 10, 2015Talla
Wannan lamari ya biyo bayan da wani ɗan jarida mai yi aikin bincike,ya fitar da wani faifan bidiyio wanda ke nuna ƙarara alƙalan sun amince suka karɓi cin hanci.Ɗan jaridar mai sunan Anas Aremeyaw Anas ya miƙa hotunan bidiyion ga mahukunta shari'a na ƙasar wanda a ciki alƙalai da dama ke da hanu a cikin lamarin na karɓar na goro.
A shekarun 2014 a rahoton da ƙugiyar yaƙi da cin hacin ta Tranparency Interational ta bayyana, Ghana ita ce ta 61 cikin ƙasashe 175 a duniya a kan batu na yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa.