1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fallasa jiga-jigan masu kauce biyan haraji

Uwais Abubakar Idris/SBApril 4, 2016

Lamura suna kara dagule wa shugaban majalisar dattawa ta Najeriya bisa bankado zargin kauce biyan kudaden haraji.

https://p.dw.com/p/1IPCl
Nigeria Bukola Saraki
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A Najeriya ambato sunan shugaban majalisar datawan kasar Sanata Bukola Saraki a cikin jerin ‘yan siyasa da shugabanin kasashen da ke kokarin hallata kudaden haram a rahoton da cibiyar binciken kwakwaf ta Panama Papers ta yi ya sanya duba ci gaba da zargin kin bayyana kadarori da masu rike da mukamman siyasa ke fuskanta a kasar.

Wannan zargi na kokarin hallata kudadden haramun da cibiyar ta bankado wanda ya nuna ya shafi shugabanin kasashen duniya har 12 da ‘yan siyasa da ma masu rike da madafan iko guda 128 a kasashen da dama, a zahiri na nuna yadda wannan batu na hallata kudadden haramun ke kara kazanta duk da matakan da aka shimfida na hana hakan.

Panama Papers Mossack Fonseca
Hoto: picture-alliance/dpa/J.F.Frey

Binciken ya bankado cewar akwai kadarori hudu mallakar shugaban majalisar datawa ta Najeriya Sanata Bukola Saraki wadanda ba sa cikin kadaraorin da kotun da'ar ma'aikata ke tuhumarsa da kin bayyanawa, abin da ya sabawa doka a Najeriya. Wannan dai na nuna yadda allura ta bankado garma a wannan batu. Comrade Nasiru Kabiru jigo a kungiyoyin da ke fafutukar yaki da cin hanci ya ce rashin koyon darasi daga abin da ya faru a baya.

Irin yadda wannan cibiya ta Panama Papers ta tona asirin kokarin rufa-rufa da hallata kudadden haram ga shugabanin kasashen duniya ciki har da na Rasha na zama abu mai daure kai, musamman sanin cewa kasashen da ake ganin sun ci gaba ba sa wannan aika-aika.

Deutschland Titelseite Süddeutsche Zeitung Panama Papers
Hoto: DW/B. Kling

A yayain da wannan ke faruwa za a zura ido a ga inda za ta kaya duk da musanta duk wani zargi da Sanata Saraki ya yi ta hannun lauyoyinsa.