1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara azumin watan Ramadan a wasu ƙasashen musulmi

September 12, 2007
https://p.dw.com/p/BuBc

Yau a wasu ƙasashen musulmi na dunia a ka fara azumin watan Ramadan.

Rahottani daga Nigeria da Niger sun tabbatar da cewar mafi yawan musulmi a wannan ƙasashen sun tashi da azumin farko a yau laraba.

Saidai a ƙasar Indonesia, wadda ta fi yawan musulmi a dunia, da kuma wasu ƙasashen larabawa, da su ka haɗa da Saudi Arabia , Koweit, Bahrein, Qatar, da haɗɗaɗiyar Daular larabawa, sai gobe a ke fara azumin na Ramadan.

Kamar ko wace shekara, an ka samu rabuwar kanu a game da farkon wannan wata mai tsarki na addinin musulunci.