1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara binciken kan lalata wasu faifayen bidiyo da CIA ta yi

December 9, 2007
https://p.dw.com/p/CZHk
Ma´aikatar shari´a ta Amirka ta ba da sanarwar fara gudanar da binciken farko kan wasu faifayen bidiyo da hukumar leƙen asiri CIA ta lalata su. Bidiyon na nuni da yadda ake yiwa wasu mutane da ake zargi da ta´addanci tambayoyi. Za´a yi amfani da sakamakon wannan binciken da wanda hukumar CIA ita ta yi don tabbatar da ko akwai isassun shaidu na kaddamar da wani gagarumin bincike. Daraktan hukumar CIA Michael Hayden ya yi maraba da wannan shawara. Hayden ya ce an lalata bidiyon ne don kare jami´an da suka yi tambayoyi. To amma tambayar da ake ita ce ko faifayen na ɗauke da wasu tsauraran matakai na yiwa mai laifi tambayoyi.