1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara bukukuwan zagayowar shekara guda da aukuwar Tsunami

December 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvFE

Shekara daya daidai bayan aukuwar mummunar girgizar kasar nan ta karkashin teku, wato Tsunami, wadanda suka tsira da rayukansu daga wannan bala´i da ya addabi yankin kudanci da kudu maso gabashin Asiya, sun hallara a kasar Tahiland don yin bukin tunawa da wadanda bala´in ya rutsa da su. An kawata wurare da dama na gabar tekun Thailand din da tare da ajiye furanni da kandura da kuma wasu kwale-kwale da aka yi musu fenti launuka dabam-dabam. Wasu ´yan yawan shakatawa a yankin sun shiga cikin bukin addu´o´in na zagayowar shekara daya da aukuwar wannan balí daga Indallahi. A halin da ake ciki hukumomi a kasashen Sri Lanka da na lardin Aceh a Indonesia sun ba da alkaluman masu rikitarwa game da aikin sake gina wadannan yankuna da kuma ci-gaban da aka samu a shirin samar da zaman lafiya da ´yan tawaye. Wakilin MDD na musamman a yankunan dake fama da bala´in na Tsunami kuma tsohon shugaban Amirka Bill Clinton ya bayyana taimakon sake gina yankunan da cewa babban kalubale ne.