1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara gudanar da zaben shugaban kasar Chadi

May 3, 2006
https://p.dw.com/p/Buzm

A yau a kasar Chadi ake gudanar da wani zabe da ake kace-nace akai wanda bisa ga dukkan alamu zai ba shugaba mai ci Idriss Deby damar yin tazarce. Jam´iyun adawa sun kauracewa zaben suna masu zargin cewa za´a tabka magudi a ciki. Su ma ´yan tawaye sun yi barazanar hana gudanar da zaben. ´yan takara 5 ciki har da shugaba Deby suka tsaya takarar neman kujerar shugaban kasa, to amma manyan jam´iyun adawa sun kaurace masa saboda canje canjen da aka yiwa kundin tsarin mulkin kasar a bara, wanda ya bawa shugaba Deby damar tsayawa takara don nema wani sabon wa´adi karo na 3. A shekarar 1990 Deby wanda shi ne tsohon hafsan hafsoshin sojin kasar ya karbe mulki a Chadi wadda ta taba zama karkashin mulkin mallakar Faransa. Masu sukar lamirin sa na zargin cewa mulkin sa na kusan shekaru 16 na tattare da cin hanci da rashawa. Suna kuma zarginsa da mulki irin na fir´aunanci.