1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN FARA MUHAWARA KANN ZABEN SHUGABAN KASAR JAMUS A CIKIN WATAN MAYU

Yahaya AhmedJanuary 5, 2004
https://p.dw.com/p/Bvmm

A cikin wannan shekarar ne za a gudanad da zaben shugaban kasa a nan Jamus. Wannan zaben dai, ba zabe ne na gama gari ba, kamar zaben `yan majalisa da na shugaban gwamnati. Ana gudanad da wannan zaben ne a majalisun tarayya, inda `yan majalisar dokoki da ta dattijai ne kawai za su ka da kuri'a. A halin yanzu kuwa, jam'iyyun adawa na CDU da CSU ne ke da rinjayi a majalisar dattijai. Idan ko aka hada yawan wakilan da suke da su a majalisar dokoki, sai a ga cewa su ne za su sami rinjayin kuri'u. Sabili da hakan ne kuwa ake hasashen cewa, sabon shugaban kasar da za a zaba, daga wadannan jam'iyyun zai fito.

Jam'iyyar SPD, wadda shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder ke jagorancinta, ita kadai ba za ta iya taka wata muhimmiyar rawar gani a wannan takarar ba. Wannan dai na daya daga cikin dalilan da ya sa har ila yau, ba ta fid da dan takararta ba tukuna. Watakila ma, ba za ta tura kowa ba a takarar zaben. Shugaban gwamnati Gerhard Schröder dai ya yi kishin-kishin haka din, yayin da ya bayyana cewa, zai fi gwammace wa samun mace ta gaji wannan mukamin na shugaban kasa daga Johannes Rau. A shirye ma yake ya goyi bayan `yan takara mace, daga jam'iyyun adawa.

A ganin manazarta al'amuran yau da kullum dai, shugaba Schröder na matashiya ne da Angela Merkel, shugaban jam'iyyar CDU, wadda ita kadai ce wata mace, da a halin yanzu za ta iya samun karbuwa, idan ta shiga wannan takarar. Idan ko hakan ya samu, to ya kau da babban kalubale ke nan da zai huskanta, a zaben shugaban gwamnati da na majalsar dokoki da za a yi a cikin sghekara ta 2006. Amma bisa dukkan alamu, wannan dabarar tasa ba za ta ci nasara ba. Saboda ita ma Merkel, tana begen shiga takarar zaben shugaban gwamnati ne, karkashin tutar jam'iyyarta. In ko ta sami nasara, ita ce za ta kasance farkon shugaba mace, ta gwamnatin tarayyar Jamus. Wannan kuwa ya fi mata muhimmanci, da gadar Johannes Rau a fadar shugaban kasa kawai.

Amma a bangaren jam'iyyar ta CDU ma, akwai rukunai da yawa da suka fi goyoyn bayan tsai da Wolfgang Schäuble, tamkar dan takarar jam'iyyar a zaben shugaban kasar da za a yi a a watan Mayun. Sai dai babu kyakyawar dangantaka tsakanin shi Schäuble din da Merkel, duk da kasancewarsu cikin jam'iyya daya. Hakan dai ya janyo wata baraka tsakanin `yan jam'iyyar ta CDU. Wani bangaren `yan jam'iyyar dai na ganin cewa, shugaban Hukumar Kula da Yanayi ta Majalisar dinkin Duniya, Klaus Töpfer ne zai fi cancantar tsayawa takara karkashin tutar CDU. Ana nan dai ana ta ce-ce ku ce, a kan wanda zai gaji Johannes Rau, idan ya sauka daga mukaminsa a cikin watan Mayu mai zuwa.

Har ila yaui dai, daya jam'iyyar adawar ta FDP, ba ta fito fili ta nuna matsayinta ba tukuna. Ana yada rade-radin cewa, mai yiwuwa ne ta tsai da nata dan takarar. Sai dai tun kafin zaben ma, `yan jam'iyyar sun san ba za su cim ma wata nasara ba. Sabili da hakan ne kuwa duk sauran jam'iyyun siyasan ke neman shawo kansu su goyi bayan dan takarar da za su gabatar.

To ana nan dai ana ci gaba da muhawarar. A kashin gaskiya, wannan mukamin na shugaba kasa a nan Jamus, mukami ne na wakilci kawai. Shugaban kasan ba shi da cikakken iko kamar shugaban gwamnatin tarayya. Sabili da haka ne kuwa, wasu masharhanta ke ganin cewa, jam'iyyun siyasan na wuce gona da iri, da yadda suke ta gudanad da wannan muhawarar ba kakkautawa.

Abu daya ne kawai ake da tabbacinsa a halin yanzu. Wato a ran 23 da 3 ga watan Mayu, majalisun tarayya za su zabi sabon shugaban kasa.