1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN FARA TARO KAN AFGHANISTAN A BIRNIN BERLIN

YAHAYA AHMEDMarch 30, 2004

Taron dai, zai dukufa ne kan tattauna batun bai wa Afghanistan taimako. Wakilai daga kasashe fiye da 50 ne ke halartar tattaunawar a birnin Berlin. Kungiyar NATO, da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Hadin Kan Turai, su ma sun tura wakilansu.

https://p.dw.com/p/Bvkx
Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan da shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Gerhard Schröder
Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan da shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Gerhard SchröderHoto: AP

A karo na 3, Jamus za ta karbi bakwancin taron kasa da kasa kan ba da tallafi ga kasar Afghanistan. Ban da dai wakilan kasar ta Afghanistan, akwai wakilan kasashe fiye 50 da za su halarci taron, wanda za a fara yau a birnin Berlin. Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar NATO, da kuma kungiyar Hadin Kan Turai, su ma sun tura wakilansu a gun taron. Game da muhimmancin karbar bakwancin taron da Jamus ta yi dai, shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder ya bayyana cewa:-

"Hakan na alamta huldar dangantaka ne da ke tsakanin Jamus da Afghanistan. Tana kuma nuna kokarin da Jamus ke yi ne na na ganin cewa an cim ma nasara, wajen sake gina kasar ta Afghanistan."

Jamus dai, ta ce a shirye take ta tallafa wa yunkurin da gamayyar kasa da kasa ke yi na sake gina kasar. Ban da dai taimakon kudi, Jamus na kuma da kwararrun ma’aikata da kuma sojoji a kasar. Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, a cikin shekaru 4 masu zuwa, za ta ware kudi kimanin Euro miliyan dari 3 da 20 don bai wa Afghanistan din taimako. Shugaban kasar ta Afghanistan, Hamid Karzai, ya nuna gamsuwarsa da irin taimakon da Jamus ke bai wa kasarsa da cewar:-

"Taimakon da Jamus ke bayarwa, a matsayinta na karbar bakwancin wannan taron, zai bunkasa yunkurin da ake yi na tabbatad da zaman lafiya a Afghanistan. Sakamakon hakan dai shi ne kwanciyar hankali da kuma da kuma amincewa da hukumarmu. Shi ne kuma abin da zai ba mu damar gudanad da zaben shugaban kasa da na `yan majalisa."

Taimakon da gamayyar kasa da kasa za ta bai wa Afghanistan dai, shi ne zai tabbatad da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. In ko babu kwanciyar hankali, ba za a sami ci gaba ba. Taron dai ba zai takaita zamansa kan yin karo-karon kudi ne kawai ba. Ci gaban kafofin siyasan kasar, da kuma muhimman zabukan da aka shirya yi a cikin watan Satumba mai zuwa na cikin muhimman batutuwan da za yi shawarwari a kansu a gun taron. Batun tabbatad da tsaro a kasar kuma, na daya daga cikin muhimman jigogin da za a tattauna a kansu. A cikin watan Fabrairun da ya gabata dai, ma’aikatan ba da taimakon agaji daga ketare 11 ne suka rasa rayukansu, a tashe-tashen hankullan da ake ta yi a kasar.

Gamayyar kasa da kasa dai, na bukatar ganin cewa, gwamnatin Afghanistan din, ta tabbatad da samun zaman lafiya a kasar, sa’annan kuma ta fatattaki masu fataucin miyagun kwayoyi da kuma rage angizon da madugan kungoyoyi daban-daban na kasar ke da shi. Amma a ganin shugaba Schröder, kasar kadai ba za ta iya cim ma wannan gurin sai an ba ta tallafi daga ketare. Ya kara da cewa:-

"Wannan shi ne dalilinmu na kara bai wa kasar taimako, don ta iya ci gaba a hanyar samad da zaman lafiya a yankin, da kuma a wasu yankuna na ketare."

A zahiri dai, shugaba Hamid Karzai ya san cewa, kasarsa ta dogara ne kacokan kan dakarun ketare dubu 6 da aka girke can, don tabbatad da tsaro. Ya dai bayyana cewa, a cikin shekaru 7 masu zuwa, kasar za ta bukaci taimakon kudi kimanin dola biliyan 27. Game da manufofin da kasarsa ta sanya a gaba a cikin shekaru 10 masu zuwa kuwa, shugaba Hamid Karzai ya bayyana cewa:-

"Manufarmu ce, mu inganta halin rayuwar jama’ar Afghanistan kafin shekara ta 2014, inda za a sami cikakken zaman lafiya da kuma bunkasar tafarkin dimukradiyya. Muna son mu zamo kasar da take tsaye kan kafafunta, wadda kuma ba za ta dora wa abokanta da sauran duniya wani nauyi ba."

A halin da ake ciki yanzu dai, Afghanistan na bukatar taimako. A cikin kwanaki biyu da za a yi wannan taron a birnin Berlin, ababa biyu ne za a fi mai da hankali a kansu. Na daya shi ne irin taimakon da gamayyar kasa da kasa za ta iya ba ta. Na biyu kuma, shi ne irin rawar da Afghnaistan din za ta iya takawa da kanta.