1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara taron hadin kan kasa a Nigeria

June 26, 2007
https://p.dw.com/p/BuHr

Mataimakin shugaban kasar Nigeria, Dr. Good Luck Jonathan ya kaddamar da taron ganawa da wasu daga cikin shugabannin jam´iyyun adawa na kasar.Tattaunawar tazo ne a kokarin da sabon shugaban Nigeria keyi ne na ganin an kafa gwamnatin hadaka, da zata samu karbuwa a tsakanin yan kasar.Jam´iyyun adawa na kasar dai na sukar zaben daya bawa Alh Umaru Musa Yar´adua nasara ne da cewa yana cike da magudi ne da kuma aringizon kuri´u. Daga cikin wakilan jam´iyyun adawa dake halartar taron na yau, akwai wakilan jam´iyyun ANPP da AC.